Learning by Ear - Ji Ka Ƙaru
“Learning by Ear - Ji Ka Ƙaru“ sabon shiri ne na Deutsche Welle, da zai yi ƙoƙarin matso da ilimi kusa da mabuƙata dake wannan nahiya
Learning by Ear - Ji Ka Ƙaru - Fasahar Samun Nasara a Afirka
Ilimi shine ginshikin ci-gaban nahiyar Afrika. Sai dai akwai karancin makarantu da jami'o'i. “Learning by Ear - Ji Ka Ƙaru“ sabon shiri ne na Deutsche Welle, da zai yi ƙoƙarin matso da ilimi kusa da mabuƙata dake wannan nahiya.
Ana samun ci-gaba a harkokin rayuwa a Afrika. Amfani da yanar gizo (Internet) da wayar tangaraho na tafi da gidanka (Mobile) wajen sadarwa, yana daɗa karuwa, sai dai duk da haka har yanzu akwai dubban mutane da aka yanke daga cin moriyar waɗannan na'urori na zamani, dake da nasaba da ci-gaban duniya. Matasa a Afirka na ci-gaba da neman gurbi a wannan yanayi, wanda zai jagorance su zuwa samun nasara a irin ayyukan da zasu yi ko kuma irin karatu da za su yi. Alal misali waɗanne irin dama suke da ita na neman ilimi ko kuma karatu ta yanar gizo? Da yawa na tambayan irin dama da suke da ita na cin moriyar wannan sabon yanayi da duniya ke ciki. Kazalika dubban yara matasa na neman yin karatu a Turai, sai dai ba su san mene ne ke jiransu a can ba.
Ilimantarwa
Wannan sabon shiri na Learning by Ear - Ji Ka Ƙaru, zai kalubalanci waɗannan matsaloli ta hanyar ilimantarwa da nishaɗantarwa. Za a gabatar muku da shirye-shirye da suka haɗa da rahotanni, wasannin kwaikwayo na rediyo da shirye-shiryen nishaɗantarwa. Shirin Learning by Ear - Ji Ka Ƙaru, zai taimaka wa masu sauraro samun fasahar zamani domin cimma nasara a Afirka.
Marubuta na nahiyar Afirka ne za su shirya waɗannan shirye-shirye tare da haɗin kan ma'aikatan Deutsche Welle. Za a iya samun shirin Learning by Ear - Ji Ka Ƙaru a ko'ina cikin harsuna masu yawa: Ingilishi, Kiswahili, Faransanci, Hausa, harshen Portugal da harshen Habasha, a tashar rediyon Deutsche Welle ta gajeren zango da kumbon satalait. Akwai tashoshin rediyo sama da 200 daga Afirka, da za su sake yaɗa waɗannan shirye-shiryen, a sassa daban-daban na Afirka. Kazalika ana iya samun shirin ta yanar gizo, a adreshin wannan tashar rediyo. Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ce ta ɗauki nauyin shirin.












